Dangane da wani rahoto na yan'sanda, wata ta tsinci kanta a yayin da maza 5 suka yi mata fyade suka yarda ita a tashar mota.Koda yake bata iya tunawa da abin da ya faru ba.Dangane da binciken, likitoci sun ce anyi mata fyaden ne akai-akai(layi) kuma dangane da binciken nasu sun gano akwai sinadarin ROHYPNOL a jininta. ROHYPNOL:sabuwar hanya ce ta amfani dashi wajen yiwa mata fyade. Hakika wata karamar kwaya ce wadda masu yiwa mata fyade suke amfani da ita a wajen bukukuwa. Ita dai wannan kwaya tana sa hankali ya gushe,koda an yiwa mace fyade bazata sami ciki ba. Mummunan labari akan kwayar shine ita illarta bawai na lokaci ne ba,tana zama dundundun a jikin dan adam. Duk wata mace da take shan wannan kwayar bazata dauki cikiba, wannan kwayar ana zaluntar mata ta hanyar saka musu ita cikin abinsha kamar lemo, idan aka sawa mace to a wannan daren bazata iya tunawa da abin daya faruba. Kwayar ROHYPNOL tana narkewa acikin abin sha da sauri,kuma bata da dandano,bata chanja launi acikin lemo, shi yasa ganeta yana da wuya. Ita wannan kwaya ana samunta a makarantun kiwon lafiyar dabbobi da kuma jami'o'in kula da lafiya. Tana da saukin samu kuma a halin yanzu da muke ciki a jami'o'in da muke dasu a kasarnan ta zama ruwan dare, aAbin mamaki shine akwai ta yanar gizo_gizo masu ilimantar da mutane yadda ake amfani da wannan kwayar. Mata kuyi hattara idan kun fita da samarinku karku yarda ku bar abinshanku kan tebur kuje wata sabgar. Ko kuma a wajen sha'ani ku sayi naku abin shan, kuma ku tabbatar da cewa abin sha na kwalba ko gwangwani a rufe yake kafin amfani dashi,kar ku ko dandana abin shan wani.MATA sai a kula.
No comments:
Post a Comment