Shugaban Jamiyar APC na kasa Comrade Adams Oshiomole da mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR da sauran yan tawagar su sun kai ziyarar zawarci gidan Mai Girma tsohon Gwamnan Jihar Mallam Ibrahim Shekarau da dubban jama'ar sa.
A cikin jama'ar Mallam Shekarau akwai yan takarar gwamnan guda 6, da Mataimakin Shugaban Jamiyar PDP na jihar Kano, da sakataren sa, da shugabar mata da shigaban matasa da sauran su. Haka kuma akwai tsofaffin yan majalisu, da kwamishinoni gwamnayin Mallam Shekarau da saura manyan magoya bayan sa.
Ana sa ran a gobe ne Mallam Ibrahim Shekarau zasu yi gangamin ficewa daga jam'iyar PDP domin chanza sheka zuwa ta APC.
No comments:
Post a Comment